<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Mu Bubbuɗe Zukatanmu LW338</title>
<lyrics>[V1]
 1) Mu bubbuɗe zukatanmu
 Ga Ubangiji Allah,
 Mu miƙa mar hadayarmu,
 Mu yi masa sujada
 Domin yalwar wadatarsa
 Da duk amfanin gona.
 Mun gode wa Ubangiji
 Domin kyautansa duka.

[V2]
 2) Mun girbe dukan gonaki,
 Ga dawa cikin rumbu.
 Mun tara dukan amfani
 Na aikin hannuwanmu.
 Wannan ne fa abincinmu
 Na rai a wannan duniya.
 Kullum fa ka ciyad da mu
 Da abinci na ruhu.

[V3]
 3) Mun yi wahalar damuna,
 Mun sha gajiya ainun,
 Amma a ƙarshen yini fa
 Ka ba mu damar hutu.
 Ka sa mu zama zaƃaƃƃu
 Na ƴaƴan fari naka,
 Mu cika aikinka a nan,
 Mu shiga hutu naka.

[V4]
 4) Ƙasar can mai albarka ce,
 Ƙasa ta mulkin Allah.
 Can dai akwai itacen rai,
 Da kuma kogin Allah.
 Duk tsarkaka sun taru can,
 Mu kuma za mu bi su,
 Mu yi ta yabon Allah can,
 Don ya albarkace mu.</lyrics>
<hymn_number>338</hymn_number>
</song>